An fara: Tinubu na bukatar addu'a, cewar Gwamna Masari, duba dalili


Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bukaci ’yan Najeriya da su dage wajen yi wa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu addu’a. Jaridar Aminiya ta rahoto
.

Masari ya bayyana haka ne wajen taron buda baki na musamman da aka shirya gidan gwamnatin Katsina, inda ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya sanya aka yi zabe lafiya.

A cewar gwamnan, zababben shugaban kasar, yana gudanar da taron addu’a na musamman duk shekara a watan Ramadan.

Ya ce: “Taron wannan shekarar an shirya shi don gode wa Allah kan nasarar da aka samu a zaben da ya gudana a fadin kasar nan.

“Ba abin da za mu yi face mu gode wa Allah kan nasarar da muka samu a Katsina da Najeriya.

“Wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka hadu da shugabannin Addini, shugabannin gargajiya, ma’aikatan gwamnati da masu ruwa da tsaki.

“Akwai sabon shugaban kasa da aka zaba, yana bukatar addu’a, abu mafi muhimmanci shi ne mutane sun gane bayan zaben shugabanni suna kuma bukatar addu’a.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN