Zaben Kebbi da Adamawa: "Mun fi kowa murnar a kammala zabe’


Najeriya, tuni wasu `yan takara da ke dakon a kammala zabensu suka yi maraba da sanarwar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC, wadda ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu mai zuwa don kammala zaben gwamnoni da na`yan majalisun dokoki a wasu sassan kasar.

Sanarwa INEC din ta kawo karshen dogon zaman jiran da al`umomin yankunan da zaben ya shafa da kuma `yan takara ke yi. BBC ta rahoto.

Jihar Adamawa da Kebbi su ne jihohi biyu rak da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriyar.

Tsohon ministan lafiya da harkokin wajen Najeriya kuma jigo a kwamitin yakin neman zaben gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a Adamawa, Dr Idi Hong, ya shaida wa BBC cewa, tsayar da ranar sake zaben za ta ba su damar sake shiri har su sake zuwa wuraren da aka soke zabensu don sake yada manufofinsu.

Ya ce, “ Dama mu jam’iyyar PDP masu bin doka ne don haka za mu jira ranar da aka tsayar don sake zaben nan, idan aka yi zaben nan za a gane bambanci.”

A jihar Kebbi ma zaben gwamnan da aka yi a zagayen farko, kamar yadda hukumar zabe ta ce bai kammala ba, saboda ratar kuri`a 45,000 da doriya da dan takarar gwamna na jam`iyyar APC ya bai wa takwaransa na PDP ba ta zarta yawan masu katin zabe 91, 000 da doriya da ke yankunan da aka soke zabe ba.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam`iyyar APC, Alhaji Kabiru Sani Jahin, ya shaida wa BBC cewa suna maraba da ranar kammala zaben.

Ya ce, “ Ya mana dadi kwarai da gaske saboda mu ‘yan jam’iyyar APC mu ke kan gaba a zaben da aka yi, don haka mun fi kowa farin cikin a sake wannan zaben.”

Bayan zaben gwamnan da za a kammala a jihohi biyun, za kuma a karasa na`yan majalisar dattawa a gundumar sanata biyar a wasu sassan Najeriyar.

Sannan akwai kujerar majalisar wakilai 31 da su ma za a kammala zaben nasu.

Sai kuma kujerar majalisar dokoki ta jiha guda 58 da su ma suke dakon a karasa zaben nasu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN