Type Here to Get Search Results !

Main event

Matar aure ta kwara wa matar makwabci ruwan zafi a jihar arewa


Wata matar aure, Nafisa Abbas,  a ranar Juma’a ta gurfana a gaban wata kotun yanki mai daraja ta daya da ke Karu, Abuja, bisa zargin ta da yi wa makwabciyarta rauni.

 ‘Yan sanda sun tuhumi Nafisa, mai shekaru 20, da laifin haddasa mummunan rauni da kuma tayar da hankali.

 Sai dai wanda ake tuhumar ta musanta aikata laifin.

 Mai gabatar da kara, Mista Olanrewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa a wani lokaci a watan Disambar 2022, wadda ake kara ta zuba wa makwabciyarta ruwan zafi da wake, wanda ya yi sanadin jikkatar ta.

 Osho ta ce wadda ake zargin ta je dakin girkin makwabcinta ne domin debo ruwa don yi wa jaririyarta wanka a lokacin da lamarin ya faru.

 Ta ce lamarin ya faru ne a gidansu da ke bayan Cocin ECWA da ke Karu a Abuja.

 Osho ta ce an kawo wanda ake kara ofishin ‘yan sanda na Karu a lokuta da dama saboda tada hankalin jama’a, kuma ‘yan sanda sun gargade ta da ta daina aikata laifin.

 Laifukan da ake zargin sun ci karo da tanadin sashe na 248(2) da na 114 na kundin laifuffuka.

 Alkalin kotun, Malam Umar Mayana, ya bayar da belin Nafisa a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu masu tsaya mata.

 Alkalin kotun ya dage sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Maris domin ci gaba da sauraron karar.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies