Babban Bankin Najeriya (CBN), ya tabbatar da kwashe takardun kudi daga rumbun ajiyarsa zuwa bankunan kasuwanci a fadin kasar.
Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito. A cewar sanarwar da Dr Isa AbdulMumin, Mukaddashin Daraktan Sadarwa na Kamfanin na CBN ya fitar, ya ce wani yunkuri ne na hadin gwiwa na ganin an sassauta yaduwar takardun kudin a cikin al'umma.
AbdulMumin ya ce, bankin na CBN ya kuma umarci dukkan bankunan kasuwanci da su bude aiki a ranakun Asabar da Lahadi domin biyan bukatun abokan huldar su.
Ya ce Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da kansa zai sa ido kan yadda bankunan kasuwanci ke bin umarnin.
A cewarsa, an samu makudan kudade a bangarori daban-daban da bankunan suka samu don ci gaba da rabawa ga kwastomominsu.
“CBN ta kuma umurci dukkan bankunan da su yi lodin ATM dinsu tare da gudanar da ayyuka na zahiri a dakunan banki a karshen mako.
"Rassan bankunan kasuwanci za su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi don biyan bukatun abokan ciniki," in ji shi.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri domin nan ba da dadewa ba za a samu saukin halin da ake ciki.
BY ISYAKU.COM
Madalla ka ji maganar hankali. A raba wa jama'a kudi rayuwa ta yi sauki don allah
ReplyDeleteKai da gaske ne kuwa?
ReplyDeleteTap aikin banki har ranar Asabar da Lahadi kuma
ReplyDelete