Matashi Ya Sauya Daga Kaura Zuwa Hadadden Gaye, Bidiyon Ya Girgiza Yanar Gizo


Wani mutumi da ya wallafa bidiyon sauyawarsa a TikTok ya yi fice kuma ya haddasa cece-kuce a dandalin. Rahotun Legit Hausa.

Bayan ganin bidiyon wanda @trickyfreshy ya wallafa, wasu masu amfani da TikTok sun gaza yarda da mutumin duba ga yadda ya sauya ya yi haske a sabbin hotunansa idan aka kwatanta da tsoffin.

Shakka babu, manufar mutumin shine nuna yadda jikinsa ya sauya cikin shekaru biyar da suka gabata

Sai dai kuma ya sauya sosai ta yadda mabiyansa da dama a TikTok suka garzaya sashin sharhi don tambayarsa yadda aka yi ya cimma wannan sabon kamanni nasa.

A tsohon hoton, mutumin na dauke da fuska irin na kauraye da yanayin jikinsa da ya yi kama da tsoho, sai dai kuma, ya sauya a sabbin hotunan.

Yanzu ya koma matashi shar da shi ga fatar jikinsa tana sheki wanda gaba daya ya banbanta da yanayinsa na shekaru biyar da suka gabata.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN