Farashin kayan hatsi da dabbobi ya tashi sama a ranar Talata, 14 ga watan Maris a kasuwar mako na Iware da ke jihar Taraba yayin da tsoffin kudade suka bazu. Legit ya wallafa.
Daily Trust ta rahoto cewa yan kasuwa a kasuwar da ke ci duk ranar Talata sun karbi tsoffin kudade.
An tattaro cewa hakan ya sa an samu kari a farashin kayan hatsi da dabbobi a kasuwar.
A makon jiya, an siyar da kayan hatsi da dabbobi a farashi mai rahuda saboda rikicin tsabar kudi amma lamarin ya sauya a wannan Talatar kasancewar an karbi tsoffin kudi a kasuwar.
Yadda farashin kayayyaki yake tsakanin makon jiya da yanzu
An siyar da buhun masara yar 100kg kan N14,000 a makon jiya amma a jiya Talata N17, 000 aka siyar da shi.
Buhun shinkafa shanshara da aka siyar N16,000 a makon jiya ya kasance N18,000 zuwa N20,000 a jiya Talata, rahoton Aminiya.
Bincike ya kuma bayyana cewa babban saniya da aka siyar N270,000 da tsabar kudi a makon jiya yanzu ya koma N320,000.
Wasu yan kasuwa sun bayyana cewa karbar tsoffin kudi da aka yi a kasuwar ya bunkasa harkokin kasuwanci.
Wani dan kasuwa, Sani Faruk, ya bayyanawa jaridar cewa a makonnin Da suka gabata, masu siyan kayayyaki yan kadan ne suka fito kasuwa saboda karancin tsabar kudi, wanda hakan yasa dole aka karya farashin kayayyaki a kasuwar.
BY ISYAKU.COM