Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa daliban da ke da shekaru takwas da tara da 12 da kuma 14 ‘yan uwan juna ne daga uba daya.
ASP Mahid Abubakar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Gombe.
Abubakar ya ce wanda ake zargin, Abubakar Muhammed an kama shi ne da laifin yin lalata da daliban yara mata.
Kakakin ‘yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 7 ga watan Maris da misalin karfe 11 na safe biyo bayan korafe-korafen da mahaifin daliban, Adamu Ali ya yi wanda ya ce an yi lalata da su ne tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
“Wanda ake zargin da ke zaune a unguwar Malam-inna, Gombe, ya aikata laifin ne a makarantar Islamiyya da ke unguwarsu daya.
“An kai wadanda abin ya shafa asibiti domin a duba lafiyarsu,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.
A wani labarin kuma, Abubakar ya ce an kuma kama wasu mutane uku da ake zargi da lalata da wasu ‘yan uwa mata uku masu shekaru 12, 15 da 17.
Ya ce mahaifin ‘yan matan Aliyu Adamu na Malam inna quarters da kuma wani Alhaji Abba wanda ke aiki da Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa (NHRC) Jihar Gombe ne suka kai karar ga ‘yan sanda.
Abubakar ya ce wadanda ake zargin, Sani Adamu, mai shekaru 50; Adamu Muhammed mai shekaru 40 da Bakura Muhammed mai shekaru 30 sun amince da aikata laifin kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kotu.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI