Karancin Naira: NLC za ta jagoranci rufe ofisoshin babban bankin Najeriya a duk reshenta ranar 29 ga watan Maris


Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta ce za ta rufe dukkan ofisoshin babban bankin Najeriya CBN a fadin kasar a ranar 29 ga watan Maris, sakamakon ci gaba da karancin kudi.

 Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya rahoto Mista Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC, ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba, yayin da yake jawabi ga manema labarai a karshen taron kwamitin tsakiya na Congress (CWC).

 Idan dai ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Maris ne kungiyar NLC ta CWC ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai wanda ya kare a ranar 20 ga watan Maris domin magance tabarbarewar kudi a halin yanzu.

 A cewar Ajaero, saboda haka, taron na CWC ya yanke shawarar shiga aikin aiwatar da sanarwar mako guda.

 “Daga ranar Juma’a, za a gudanar da taron majalisar zartaswa na kasa baki daya.

 “An riga an umurce dukkan kungiyoyin kwadago da su hada dukkan sassansu da rassansu.  A ranar Larabar mako mai zuwa, za a rufe dukkan ofisoshin Babban Bankin Najeriya a fadin kasar.

 “Za a rufe duk wani babbar bankin najeriya har sai baba ya gani.  An umurci ma’aikata da su zauna a gida kuma su shiga cikin zanga zangar, ''in ji shi.

NLC, ya tuna cewa CWC ta ba da wa’adin mako guda ga gwamnati da ta gaggauta magance matsalar rashin kudi da manufar ta jawo.

“Har yanzu lamarin kusan iri daya ne.  Har yanzu mutane suna siyan kudin mu da kudaden mu, ''in ji shi.

Ya kuma ce ba a yi wani yunkuri na rage radadin ’yan Najeriya ke fusjanta kan lamarin ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN