Dan Najeriya ya kera motar da za ta iya tashi sama a Borno


Wani fasihin injiniya a Jihar Borno, Abba Dalori, ya kera tare da hada wata mota da za ta iya tashi sama a jihar.

Jaridar Aminiya ta rahoto Abba ya kammala karatun digirinsa a Jami’ar Maiduguri, inda ya samu digiri a bangaren Injiniyanci.

Injiniya Dalori ya kwashe shekaru yana kera motar da za ta tashi da kuma tuki a kan hanya kamar yadda ya bayyana.

A cewarsa wannan kirkirar tasa ya yi amfani  ne da wasu abubuwa ma su kamar farfela guda biyu masu karfi ya sa a sama da bayan motar don taimaka mata ta samu ta tashi daga kasa zuwa sama.

Dalori ya ce yana fatan motarsa da ke iya tashi za ta zaburar da sauran matasan Najeriya don ba su kwarin gwiwar ci gaba da sha’awarsu da samar da sabbin hanyoyin ciyar da kasar su gaba wajen kere-kere.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN