Labari Mai Dadi: CBN Zai Share Hawayen 'Yan Najeriya, Ya Shirya Yi Musu Abinda Suka Dade Suna Jira Kan Tsaffin Kudi


Babban bankin Najeriya (CBN) ya kammala shirye-shirye tsaf domin sako dukkanin tsofaffin takardun kuɗi na N1,000, N500 da N200 a hannun shi zuwa ga bankuna. Rahoton Punch

Wannan matakin ana sa ran zai kawo ƙarshen watannin da ƴan Najeriya suka kwashe suna shan wahala akan sauya fasalin kuɗi da babban bankin Najeriya (CBN) yayi. Legit ya wallafa.

Wannan sabon matakin na babban bankin na zuwa ne bayan an kwashe makonni da dama tun umurnin da kotun ƙoli ta bayar na tsofaffin takardun kuɗin su cigaba da zama halastattu har sai zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

A ranar Laraba da daddare, manyan jami'an bankin CBN da na wasu bankunan, sun tabbatar da cewa gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ya bayar da umurnin cewa bankuna su fara rabawa mutane tsofaffin kuɗin daga yau (Alhamis)

A cewar sa, CBN zai fara ba bankuna tsofaffin takardun kuɗin daga ranar Alhamis. Rahoton The Nation

Godwin Emefiele ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci a ranar Laraba da yamma, inda ya gaya musu cewa babban bankin zai fara basu tsofaffin kuɗin da yake da su daga ranar Alhamis.

Majiyoyi masu ƙarfi a wajen taron sun bayyana cewa CBN zai kuma soke kayyade damar cire kuɗi da ya sanya wacce ta kwashe lokaci mai yawa.

Haka kuma, bankin CBN ya bayyana cewa daga yanzu idan kwastomomi za su kai tsofaffin kuɗin su basu buƙatar sai sun samo lambobi kamar yadda ake yi a baya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN