Type Here to Get Search Results !

Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu Kan Zargin Cewa Buhari Ba Zai Mika Mulki Ga Tinubu Ba Ranar 29 Ga Watan Mayu


Fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, 24 ga watan Maris, ta karyata rahotannin da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da niyyar mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a karshen wa'adin mulkinsa ranar 29 ga watan Mayu.

Legit ta rahoto wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ya ce, tuni shirin gwamnati na mika mulki ya yi nisa, a cewar rahoton gidan talabijin na Channels.

Fadar shugaban kasa na son sanar da cewa labarin karya ne kuma mara makama, ta kuma yi Allah wadai da jingina kalaman karya ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma yada shi.

''Ta ya zaka tallata wani iya karfinka, ka zabe shi sannan ace ba za ka mika ma sa mulku ba? Wannan tunanin marasa ilimi ne.''

Shehu bayyana kafar yada labaran da ta wallafa rahoton (ba Legit.ng ba) a matsayin ''mara sanin ya kamata'' ya kara da cewa mammalakinta ''ya dauki bangare a siyasa, hasalima ya fadi a zaben shugaban kasa.''

Daga Buhari zuwa Tinubu: Fadar Shugaban kasa ta yi bayanin shirin mika mulki
Shehu kuma cigaba da cewa a kafa kwamitin mika mulki, da ya hadar da wakilan gwamnatin Buhari da kuma gwamnati mai jiran gado ta Tinubu.

A cewarsa, kwamitin na tattaunawa kullum.

''Tuni gwamnati ta fara shirin mika mulki. Kwamitin mika mulki, da ya hadar da wakilan gwamnati mai barin gado da mai jiran gado su na tattaunawa kusan kullum don shirya yadda za a mika mulki ga gwamnatin

 Tinubu/Shettima,'' in ji shi.
''Akwai kananan kwamitoci 13 da aka fitar daga babban kwamitin, wasu, don shirya faretin sojoji da kuma raka shugaba Buhari, sun fara aikinsu ko su na daf da farawa. Zuwa yanzu, komai na tafiya dai dai kuma ba alamun tangarda.''

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN