Ta faru: Zababben ‘Dan Majalisa Ya Sha da Kyar, An Kusa Kashe Shi, An Kona Motarsa Kurmus


Aondona Dajoh wanda ya yi nasarar lashe zaben ‘dan majalisa mai wakiltar Gboko ta yamma a jihar Benuwai ya tsira da ransa da kyar. Legit ya wallafa.

The Sun ta kawo rahoto a ranar Juma’a cewa wasu miyagu sun yi nufin kashe Aondona Dajoh, sun auka masa yayin da yake tafiya a mota.

Wadannan miyagu da ba a san su ba, sun shirya masa kwantan-bauna a hanyarsa ta zuwa gida a daren Juma’a, saura kiris a hallaka 'dan siyasar.

Ko da zababben ‘dan majalisar Gboko ta yamma a majalisar dokokin Benuwai ya sha da kyar, motar da yake ciki ta kone kurmus, ta zama toka.

An rutsa Honarabul a Gyado
Tribune ta ce an aukawa wannan Bawan Allah ne a daidai yankin Gyado da ke karamar hukumar Gboko da yammacin ranar Alhamis da ta gabata.

Wata majiya ta ce dole ‘dan majalisar mai jiran gado ya rabu da motarsa, ya ari ta kare yayin da ya tabbatar da wadannan mutane za su ga bayan shi

Yan sanda sun yi magana
Da manema labarai suka tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar wannan lamari a jiya.

SP Catherine Anene ta ce babu shakka an kai wa Hon. Aondona Dajoh, duk da ya tsere ba tare da ko da rauni a jikinsa ba, amma an kona abin hawansa.

Anene ta sakon wayar salula, ta bayyana cewa Jami’an tsaro sun fara bincike a kan batun da nufin gano wadanda suka yi aika-aikan, sai a hukunta su.

A makon jiya aka yi zaben jihohi, Dajoh da ire-irensa suka lashe kujerun majalisar dokoki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN