Sako zuwa ga Jama'ar Jihar Kebbi kan Zaben da za a yi na Gwamnoni da 'yan Majalisar Jiha - Abu Najakku (Dan Bello)


Sponsored post: Salaam alaikum daukachin jama'ar jihar Kebbi. 

Ina son in yi tsokachi, in kuma ba mu shawara a kan zaben Gwamnoni da 'yan majalisa da za a yi jibi ranar sha takwas ga watan Maris, watau 18th March, 2023. 

1. Da farko dai ya kamata mu san 'yanchin mu a tafarkin dimokaradiya. Dimokaradiya ta bai wa duk wanda ya chika sharuddan tsayawa takara da ya tsaya takara, wanda kuma ke sha'awar zabe, da ya zabi duk wanda ran shi ke so, ba tare da kowache irin tsangwama ba, daga kowane mutum, ko shi waye. 

2. Domin akwai labarai da ke zuwa suna dawowa cewa gwamna da gwamnati mai ci sun rabawa Sarakuna, da Hakimai, da Dagatai, kudi  masu tarin yawa, wai domin su ciwo masu zabe a kofofin gidajen su, da runhunan zabe, da kauyukan su, da garuruwan su. 

3. Toh, wannan ba dimokaradiya ba ce. Wannan tursasawa ne, da yaudara, da zalunchi. Wannan neman fin karfi ne da cin zarafi. 

4. Ba aikin Sarki ba ne, ko Hakimi, ko Dagaci, ya ciyo ma wata jam'iyya ko dan takara zabe ba. Ko kadan, wannan ba aikin Masarautu ne ba.

5. Hakkin ko wane dan takara ne, ko jam'iyyar shi, su je su nemi goyon bayan jama'a domin a sanya mu su kuri'a, ba su labe, ko su boye bayan wani Sarki, ko Hakimi, ko Dagaci ba, su tilasta masu wai dole ne sai wata jam'iyya, ko dan takara ya yi nasara a zabe ba. 

6. Shi kan shi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai taba tilasta wa kowa ba cewa sai an zabe shi. A'a. 
A ko yaushe ya na gaya wa mutane su zabi jam'iyya ko dan takarar da su ke so.

Kuma idan za ku iya tunawa a 2015, duk da kudin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya rabawa wa jama'a, bai hana jama'a su ka zabi Buhari ba, saboda a lokachin shi Buharin jama'a ke so. 

7. Saboda haka, idan gwamna ko wata gwamnati ta ba ku kudi, ko takin zamani, ko abinci, toh ku karba, amma ku jefa wa jam'iyya, ko dan takarar da ran ku ke so. 

8. Kar mu kuskura mu karaya, ko mu ji tsoron barazana, ko bude idon da wani gwamna ko gwamnati, ko 'yan barandan su, za su yi na cire mutane daga kujerun su na Sarauta, ko wani mukami. 
Idan ma wani gwanna ya sauke ku kan mukaman ku wai don ba ku zabi jam'iyya ko dan takarar shi ba, toh gwamnan da ya yi nasara, zai maida ku kan mukaman ku cikin gaggawa. Ko wane irin mulki, ko na siyasa ne, ko na sarauta ne, Allah ya ke bada shi. 

9. Jama'a ku tambayi kan ku: mi ya sa a ka ki ba ku kudi sai yanzu? Mi ya sa ba a ba ku takin zamani ba sai yanzu? Mi ya sa a ke ba ku buhuhuwan abinci yanzu? Mi ya sa ba a ba ku kudi, da takin zamani, da buhuhuwan abinci bara ba? Mi ya sa ba a ba ku abubuwan nan ba, waccan bara? Sai yanzu da su ke son a zabe su shi ne su ke rabon kuddi a gigice? Ku tambayi gwamnatin nan da 'yan barandan ta, ina su ka samo wannan makuddan kudi da su ke raba maku? Aikin mi suka yi suka samo wannan kuddi ma su yawa haka? Wannan ai tarko ne a ke son a hada ma ku, a tauye ma ku hakkin hana ku zabin da ku ke so a tafarkin dimokaradiya. 

10. Jama'a ka da ku yarda a yaudare ku. Sarki ya zabi wanda ya ke so. Hakimi ya zabi wanda ya ke so. Ko wane Dagaci, ya zabi jam'iyya ko dan takarar da ya ke so. Sarki goma, zamani goma. Su kuma talakawa, a bar su, su zabi dan takara, ko kuma jam'iyyar da ran su ke so. Wannan ba mulkin soja ba ne, wannan lokacin dimokaradiya ne. 

11. Ka da ku bari diyan talakkawa su bude ma ku ido, su sayi mutuncin ku da kudi, su tilasta ma ku zaben jam'iyya ko dan takarar da ba ku so. 
Ku guji mayaudara, da makaryata, da azzalumai. 

12. Haka kuma idan an gama kidayan kuri'a a mazaba, to a kiyaye da nagartar takardar sakamakon zabe bayan da ko wace jam'iyya ta sanya hannu a kai. Mu tabbatar da malamin zabe ya sanya sakamako a yanar gizo da hukumar zabe, watau INEC, ta tanada. Haka kuma a yi ma akwatin zabe da sakamakon rakiya, tun da ga rumfunan zabe har sai an kai mataki na karshe. Kar a dauke ido ko da kyaftawa daga Malamin zabe da sabgar da ya ke yi, daga mataki zuwa mataki, sai an isa mataki na karshe da sahihin sakamakon zabe, sannan kuma a jira sai babban malamin zabe ya bayyana sakamako a bainar jama'a. Kowa ya tabbatar da abin da ya zaba, shi ne a ka ba shi.

13. Da ga karshe, ina yi ma dukkan mu fatar a yi zabe lafiya. Allah ya ba mu ikon zaben shuwagabannin da ke tausayin mu, masu cika alkawulla, masu rikon amana. Allah ya tabbata mana da alhairinsa. 
Allah ya ba mu rai da lafiya. 

Na ku Abu Najakku (Dan Bello)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN