Type Here to Get Search Results !

Dattijon arziki: Tinubu ya magantu kan rashin tsaro ya ce dole a daina-kashe a Najeriya


Zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kashe-kashen rashin hankali bai da hurumi a kasar nan. Legit ya wallafa.

Tinubu ya fadi hakan ne yayin da yake martani ne ga mummunan harin da yan bindiga suka kai kan ofishin yan sanda a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, jaridar The Cable ta rahoto.

A safiyar ranar Lahadi, 5 ga watan Maris ne yan bindiga suka farmaki yankin inda suka kashe shugaban yan sanda na yankin wato DPO, Kazeem Raheem, da wasu jami'an tsaro biyuu.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadimininsa, Abdulaziz Abdulaziz, a ranar Litinin, Tinubu ya bayyana cewa ya zama dole al'ummar kasar su hada kansu don cin nasara a kan wadannan makasa.
Tinubu ya ce:

"A matsayinmu na kasa, ya zama dole mu hade don cin galaba kan wadannan makasan yan ta'addan a lokaci daya.
"Bai kamata kisan rashin hankali da zalunci irin wannan ya samu hurumi a kasarmu ba."
Tinubu ya kuma ce ya kamata ayi bincike a kan kisan hakimin Maigari a jihar Kano, wanda shine mahaifin Munir Dahiru Maigari, shugaban karamar hukumar Rimin Gado, rahoton Premium Times.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies