Soja ya bindige Kwamanda har lahira, abokan aikinsa, ya kuma kashe kansa a Sokoto


Rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin ta tabbatar da shari’ar wani soja da ya harbe abokan aikinsa da kansa har lahira a sansanin ‘Forward Operations Base, Rabbah, jihar Sokoto a ranar Lahadi. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito
.

 Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig.-Gen.  Onyema Nwachukwu, ya bayyana a Abuja cewa an fara bincike kan lamarin. Daily trust ta wallafa.

 Mwachukwu ya bayyana cewa, ba za a iya tantance halin da ake ciki a yanzu ba tunda sojan da ya kashe abokan aikinsa shi ma ya harbe kansa har lahira.

 Ya kara da cewa babban jami’in runduna ta 8 (GOC) da kuma kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Northwest, Hadarin Daji Maj.-Gen.  Godwin Mutkut, da wasu manyan hafsoshi sun ziyarci wurin.

 A cewarsa, GOC ya jajantawa sojojin da suka rasa abokan aikinsu a irin wannan yanayi mara dadi.

 "Ya bukace su da su zama masu kula da 'yan uwansu kuma su ba da rahoton duk wani rashin lafiya da aka samu a tsakanin abokan aiki don hana sake faruwa.

 “Ya kuma kara musu kwarin gwiwa da su kwantar da hankula da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

 “Hukumomin Sojojin Najeriya sun damu matuka game da wannan sabon abu mai ban mamaki kuma sun kafa hukumar bincike (BOI) don bankado al’amuran da suka faru.

 "Ana hasashen cewa sakamakon binciken BOI zai taimaka wajen dakile irin wannan munanan al'amura a nan gaba," in ji Nwachukwu.  

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN