CBN ya magantu kan matsayin da ake ciki kan tsoffin Naira bayan hukuncin Kotu


Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar Talata ya bayyana cewa, bai ba da wani umarni ga bankunan kasuwanci ba kan hukuncin kotu koli na ranar Juma’ar da ta gabata na ci gaba da kashewa da ba da tsoffin Naira ba.

Idan banku manta ba, kotun kolin Najeriya ya yanke hukunci ga karar gwamnoni, inda yace za a ci gaba da ta’ammuli da tsoffin N200, N500 da N1000 har zuwa karshen watan Disamban bana.

Rahotanni sun bayyana yadda aka samu rudani tsakanin ‘yan kasuwa da bankunan kasar kan rashin cewa komai da CBN ya yi game da hukuncin kotun.

Mai magana da yawun CBN, Isa Abdulmumini ya zanta da jaridar DailyTrust, inda ya ce babban bankin bai ba da wata sanarwa a hukumance kan ci gaba da ba da tsoffin kudaden ba.

Sai dai, duk da haka wani babban ma’aikacin bankin ya shaidawa jaridar a wata tattaunawa cewa:

“Tsoffi da sabbin kudi duk sun halasta a kashe, kuma bankuna a yanzu haka suna ba kwastomomi. Kada ‘yan Najeriya su ki karbar kudi, tsoho ko sabo.”

Sai dai, kamar bankuna sun yi riga-malam masallaci, domin bincike a wasu bankunan kasar nan da aka yi ya nuna, tuni sun fara raba tsoffin kudaden ga kwastomominsu; musamman ‘yan N500 da N1000.

A Legas, wasu daga bankunan GT, Zenith da WEMA tuni suka fara sanya kudaden a injunan ciran kudi na ATM da kuma ba da kudin a kan kanta.

A bangaren wasu bankunan kuma kamar First Bank, Poliris da Unity, ba a fara ba da kudaden ba ga kwastomomi, kuma babu wani karin bayani.

Hakazalika, ‘yan kasuwa da yawa sun ki karbar wadannan kudade duk da kuwa da umarnin kotun don gudun asara idan CBN ya fadi sabanin abin da kotu yace.

Babban kantin siyayya na San-Hussein a tsakiyar jihar Gombe ba ya karbar tsoffin kudaden, inda ma’aikatan kantin suka ce umarni ne daga sama.

A bangare guda, wani mai shagon kayan masarufi a unguwar Pantami, Sani Muhammad ya ci gaba da karbar kudaden har zuwa safiyar yau Laraba 8 ga watan Maris.

Ga abin da yake cewa:

“Eh, tunda aka fada a rediyo cewa za a ci gaba da karba nima na fara, akwai uban gidana, ba zai rasa hanyar shigar da kudaden ba ko da kuwa a CBN kuma na yi magana dashi.

“Mutane suna da tsoffin kudin nan, musamman masu shigowa daga kauyuka, karbar zai taimake su wajen shigar da kudaden.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN