Type Here to Get Search Results !

An yi wa wata mata mai ciki wata 8 fyade a Abuja


Wata kotun yanki da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talatar da ta gabata ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wasu makiyaya biyu da suka amsa laifin yin garkuwa da wata mata tare da yi mata fyade a gidan gyaran hali har sai an yanke hukunci a ranar 22 ga watan Maris. NAN ya wallafa.

 Tun da farko, mai gabatar da kara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake kara, Nuru Tukurai mai shekara 21 da Yusufa Haruna Dan shekara 29 a ranar 25 ga watan Fabrairu, sun yi garkuwa da wata mata mai ciki wata takwas a gidanta da ke karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja.  Sun kai ta wani daji duk su biyun sunyi mata fyade.

 Ya ce wani Abubakar Wakili na Yaba a karamar hukumar Abaji ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sandan yankin Gwagwalada a ranar 26 ga Fabrairu.

 Yakubu ya ce, a ranar 25 ga watan Fabrairu, wadanda ke fuskantar hukuncin sun sace matar a karamar hukumar Abaji daga gidanta, inda ya kara da cewa sun kai yarinyar wani daji inda su biyu suka yi mata fyade ba tare da la’akari da cewa tana da ciki wata takwas ba.

 Mai gabatar da kara ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 96, 262, 264, 387 na kundin laifuffuka.

 Alkalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkarim, ya dage yanke hukuncin ne domin ya ga ya kuma san halin da wanda aka kashe din yake ciki. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies