CBN ya fadi dalilin kirkirar eNaira, ya ce idan aka lura za a daina kashe tsabar kudi


Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi karin haske game da eNaira da ya kaddamar, inda yace an yi sa ne don takaita kashe tsabar kudi da kuma rungumar hada-hadar kudi ta yanar gizo. Legit Hausa ya wallafa.

Samuel Giwa, mukaddashin manajan CBN na Akure ne ya ba da wannan bayanin a lokacin da ya ziyarci fadar Deji na lardin Akure, Oba Aladetoyinbo Adedelusi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Giwa ya ziyarci fadar ne domin neman goyon bayan jama’ar Ondo wajen amfani da manhajar eNaira a hada-hadarsu ta yau da kullum.

Amfanin manhajar eNaira
Da yake jawabi ga jama’a, Giwa ya ce, eNaira zai habaka wa ‘yan Najeriya hanyoyin musayar kudade, zai rage rashawa da damfara kana ya kara fadada harkar hada-hadar kudi ga ‘yan kasar.

Ya kara da cewa, eNaira ba wai kudi bane kawai ba, wata hanya ce ta kirkirar damammaki na musayar kudi da kuma saukaka hanyoyin hada-hada ga ‘yan kasar cikin sauki da tsaro.

A cewarsa:

“Babu shakka tsarin eNaira ya zama wani muhimmin ginshiki na tsarin hada-hadar kudi a Najeriya da kuma samar da wata hanya ta daban wajen hada-hada.

“Ba wai kawai za ta habaka tattalin arzikin Ondo bane, za ta habaka tattalin arzikin Najeriya baki daya; alamar ci gaba da kirkira ce, kuma za ta saukaka hanyar hada-hada cikin tsanaki da sauki.”

Hakazalika, ya yi karin haske da cewa, eNaira zai taimaka wajen rage radadin da ake fama dashi na karancin sabbin kudi, don haka ya shawari al’ummar jihar ta Ondo da su gaggauta sauke manhajar, rahoton Vanguard.

Basaraken ya godewa CBN bisa wannan jawabin tare da kira ga al'umma da su rungumi sauyin da aka samu.

Wannan ya biyo bayan karancin sabbin Naira da ake fama dashi a kasar da kuma yadda ‘yan kasar ke kokawa.

Har yanzu, ana ci gaba da kashe tsoffin takardun Naira saboda karancin sabbi da ake gani a bankunan kasar ga kuma kunci da ake ciki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN