Type Here to Get Search Results !

Main event

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun harbe jami'an tsaro NSCDC 3, a wata jiha


Wasu tsagerun ‘yan bindiga a ranar Litinin suka kashe wasu jami’an tsaro uku na hukumar NSCDC da kuma wasu fararen hula biyu a jihar Imo, Punch ta ruwaito.

An ruwaito cewa, ‘yan bindigan sun dura kasuwar Ekelsu ne da ke yankin Obiangwu na karamar hukumar Ngor Okpala ta jihar, inda suka harbe jami’an na NSCDC da mutanen biyu. Legit ta wallafa.

Ya zuwa yanzu, rahoto bai bayyana bayanan mutum biyun da aka kashe ba a tare da wadannan jami’an tsaron da ke bakin aiki.

Yadda lamarin ya faru daga bakin ganau
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa, an farmaki wadannan bayin Allah ne da sanyin safiyar yau Litinin 27 ga watan Maris.

A cewar majiyar, jami’an na NSCDC na cikin motarsu ne a lokacin da ‘yan ta’addan suka yi musu kwanton bauna tare da kashe su da wasu mutane da ke gefe.

A cewarta, yanzu dai jami’an tsaro sun mamaye yankin tare da kokarin kame duk wasu da ake zargi da aikata barnar a yankin, matasa sun shiga taitayinsu.

Har yanzu ba a tattara gawarwakin ba
Ta kuma kara da cewa, ya zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a tattara gawarwakin matattun ba daga inda hakan ya faru.

Sai dai, da aka tuntubi jami’in hulda jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye ya shaidawa The Nation cewa, lamarin ya faru ne da daren jiya Lahadi.

Kakakin NSCDC, Chimeziri Lowell bai dauki waya ba a lokacin da majiya ta so jin ta bakinsa game da lamarin.

Lamarin ya haifar da cece-kuce, inda aka ga gawarwakinjami’an a cikin kwalbatin da ke bakin titi.

Ana yawan samun aukuwar hare-hare kan jami’an tsaro a yankunan kudancin kasar nan, musamman Kudu maso Gabas.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies