Abun mamaki: Duba Gurgun da ke bara dauke da Naira miliyan 37 a aljihunsa


Wani gurgu ya fada hannun ’yan sanda sakamakon kama shi da aka yi yana bara dauke da tsabar kudi Dala 81,000 (kimanin Naira miliyon 37.3) a cikin kafafun robar da yake tafiya da su. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Gurgun dai, wanda da aka yanke wa kafa, kuma yake tafiya da kafar roba da taimakon sandar guragu an kama shi ne a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba da kuma kasar da ya fito, ya fada hannun ’yan sanda ne bisa shiga kasar da takardar biza ta ziyara.

An kama shi ne a ranar Alhamis 16 din da ta gabata, yana bara a masallatai da wuraren shakatawa kamar yadda jaridar Gulf News ta rawaito.

’Yan sandan suna zargin mabaracin gurgun da yin karya, kasancewar an samu tarin kudin boye a cikin kafarsa ta roba duk da yake yana nuna cewa shi mubukaci ne da ke neman taimakon jama’a.

Rundunar ’Yan sandan Dubai da ta yi kamun ta gargadi jama’a da kada su rudu da mabarata da suke kirkirar dabaru daban-daban don neman tausayawarsu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN