Mutum daya ya rasu, wasu da dama sun samu raunuka bayan ’yan daba sun kai farmaki a rumufunan zabe a sassan Jihar Legas. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Aminiya ta gano cewa an harbe mutum daya har lahira, wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da bata-garin suka yi dirar mikiya a wuraren zaben.
Yankunan da aka kai hare-haren sun hada da Ikota, Jakande, Ijegun, Festac da kuma Isolo.
Rikicin ya fara barkewa ne bayan bata-garin sun kutsa cikin yankin Okota, inda jam’iyyar LP ke da karfi.
Maharan sun fatattaku mutanen da suka fito yin zabe, sannan suka lalata akwatunan zabe, suka tafi da wasu.
BY ISYAKU.COM