Ta faru: An harbi ma'aikaciyar INEC —REC ya maganta


Wani dan bindiga ya harbi wata ma’aikaciyar wucin gadi ta Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Miss Glory Effion Essien, a hanyarta ta zuwa Karamar Hukumar Bakassi don gudanar da aikinta a ranar zabe. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Baturen Zaben Jihar Kuros Riba, Farfesa Gabriel Yomeri ne ya bayyana hakan inda ya ce an kai ta asibiti tana karbar magani.

Gabriel ya bayyana rashin jin dadinsa da afkuwar lamarin, sai dai ya ce ya ji dadi da harbin bai lahanta mata lakar jikinta ba.

Rahotanni dai na nuna dan bindigar da ya harbe ta a baya lokacin da take kan hanyarta ta zuwa aiki a kwale-kwale, guda ne daga cikin masu tada kayar bayan da suka addabi yankin Bakassin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN