Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kebbi INEC ta fara kudayar sakamakon kuri'un zaben Gwamna da na Majalisar dokoki da aka gudanar a jihar.
Gidan rediyon tarayya Equity FM Birnin kebbi ta labarta cewa an kammala kidayar kuri'un shida daga cikin kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar.
Kananan hukumomin sun hada da Aliero, Bunza, Kalgo, Maiyama, Suru da Zuru. Equity FM ta ce dan Takarar jam'iyar APC ke kan gaba a kananan hukumomi hudu cikin shida kawo yanzu.
Yayin da na jam'iyar PDP la lashe kananan hukumomi biyu cikin shida kawo yanzu.
Ana ci gaba da tattara tare da kidayar kuri'un sauran kananan hukumomi.
Ku kasance da mu don kawo maku sakamakon sauran kananan hukumomi da zarar INEC ta kammala kidayar....
BY ISYAKU.COM