Type Here to Get Search Results !

An Bindige Shugaban Kamfen Jam’iyyar APC, Ya Mutu Yana Kokarin Hana Ayi Murdiya


Shugaban yakin neman zaben jam’uiyyar APC a karamar hukumar Ahoada yamma a jihar Ribas, ya mutu bayan ‘yan bindiga sun harbe shi. Legit ya wallafa.

The Guardian ta kawo rahoto a safiyar Lahadi cewa an kashe Chisom Lennard wanda shi ne shugaban APC na mazabarsa ya bakunci barzahu.

An harbe Chisom Lennard ne a yayin da yake kokarin hana wasu miyagu da suka yi shigar ‘yan sanda, su na yunkurin satar kayan zabe a Ibagwa.

Kakakin kwamitin takarar Rivers APC 2023, Sogbeye Eli ya shaidawa jaridar cewa wadannan bata-gari sun bude masa wuta, nan take ya hallaka.

Maganar Sogbeye Eli
"Eh, kwarai, an kashe shugaban kwamitin neman takararmu na karamar hukumar Ahoada yamma a jihar Ribas.

An harbi Chisom ne a lokacin da yake kokarin hana wasu miyagu masu dauke da kayan ‘yan sanda satar kayan zabe.
Sun harbe shi, kuma nan take ya mutu."
- Sogbeye Eli

Marigayin yana cikin wadanda ke kan gaba wajen tallata Tonye Cole na jam’iyyar APC a Ahoda, baya ga haka yana digirinsa na PhD a jami’ar jihar Ribas.

Punch ta ce sai da aka dauke ‘dan siyasar aka yi gaba da shi, sannan sai aka ji labarin an yi amfani da bindiga an harbe shi, hakan ya yi sanadiyyar ajalinsa.

Darlington Nwauju wanda shi ne Sakataren yada labaran APC na Ribas ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da Marigayin ne, suka tafi wani wuri da shi.

“Babu wanda ya san inda suka kai shi. Da yammacin Asabar ne aka tsinci gawarsa.”
- Darlington Nwauju

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies