Kafrn hali: An damke matar da ta yi sojar gona ta sa tufafin Yar sanda ta kutsa gidan mutane


Wata mata ‘yar shekara 33 mai suna Damilola Odutola, wacce ake zargin ta yi sojar gona bayan ta yi shigar jami’ar ‘yar sanda a kokarin kutsawa wani gida a ranar Alhamis ta bayyana a gaban wata kotun Majistare ta Yaba da ke Legas.

 Odutola, wanda ba a bayar da adireshinta ba, tana fuskantar tuhume-tuhume guda biyu da suka hada da aikata laifuka da kuma tayar da hankalin jama'a. Kampani dukkanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

 Sai dai ta musanta zargin da ake mata.

 Mai gabatar da kara, ASP Rita Momah, ta shaida wa kotun cewa wadda ake kara ta aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Maris, 2021, a lamba 35a, titin Chief Collins, Uchediuno Lekki Phase 1, Legas.

 Momah ta yi zargin cewa Odutola ta shiga gidan wanda ta shigar da karar, Misis Bimpe Daramola, sanye da rigar yar sanda.

 Ta bayyana cewa Odutola da gangan ta aikata rashin gaskiya, a lokacin da ta tilasta kanta ta shiga gidan mai karar.

 Momah ta ce laifukan sun ci karo da sashe na 168 (d) na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.

 Alkalin kotun, Misis Adeola Olatubosun, ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da za su tsaya mata.

 Olatubosun ta ba da umarnin cewa dole ne wadanda za su tsaya mata su nuna shaidar biyan haraji na shekaru uku ga gwamnatin jihar Legas.

 Ta dage sauraron karar har zuwa ranar 17 ga Afrilu don ambato.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN