Yar haya ta kai mai gidan haya Lahira da gaggawa bayan ta damke mazakutarsa ta ja har ya mutu lokacin hatsaniya tsakaninsu


Wata mata ‘yar shekara 33 mai suna Ifeoma Ossai ta kashe mai gidan haya mai suna Monday Oladele mai shekaru 50 a duniya a sakamakon rashin jituwa bayan ta kama mazakutarsa sa ta ja shi har ya mutu.

 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 14 ga Maris, 2023. Shafin intelregion ya rahoto.

 A cewar PPRO, an kama Ifeoma ne biyo bayan rahoton da aka kai a hedikwatar sashin Sango-Ota.

Oyeyemi ya ce ‘wani Olaleye Taiwo ya yi wa Yan sanda bayanin cewa dan’uwansa, Oladele ya samu rashin jituwa da yar hayar nasa kan biyan kudin wutar lantarki.

 A cewar Oyeyemi a cikin rashin jituwar da aka samu, uar hayar ta damko mazakutar marigayin ta yi ta ja.

Sakamakon haka mai gidan ya fadi kasa sumamme, aka garzaya da shi babban asibitin Ota, inda likitan da ke aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

 “Bayan rahoton, DPO na Sango Ota, CSP Saleh Dahiru, ya yi gaggawar jagorantar jami’ansa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda nan take aka cafke wanda ake zargin domin gudanar da bincike.

 “Da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta yi ikirarin cewa marigayin ya bukaci ta biya kudin wutar lantarkin, amma ta dage cewa har sai an hada mata ruwan fanfo kai tsaye a bangarenta kamar yadda mai gidan ya yi alkawari kafin ta shiga, idan ba haka ba, ba za ta biya kudin wutar lantarkin ba.

 “Hakan ya haifar da hatsaniya a tsakanin su, inda wanda ake zargin ta kama mazakutar marigayin ya ja shi.

 “Marigayin ya fado daga baya, kuma an garzaya da shi asibiti amma likitan da ke bakin aiki ya ce ya mutu".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN