Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Honarabul Ahmed Mirwa Lawan ya rasa kujerarsa, ya sha kaye hannun Lawan Musa, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, mai wakiltar mazabar Nguru II, dan shekara 35. Legit ya ruwaito.
Baturen zabe na jihar, Dr Habib Muhammad, wanda ya sanar da sakamakon zaben ya ce, Musa ya samu kuri'u 6,648 inda ya kayar da kakakin majalisar na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 6,466.
Ya ce dan takarar jam'iyyar ADC ya samu kuri'u 3,023 yayin da yan takarar NNPP da APM suka samu kuri'u 14 kowannensu.
Daily Trust ta tattaro cewa Kakakin Majalisar na Yobe ya kasance a majalisar tun shekarar 2003 da aka zabe shi a matsayin dan majalisa karkashin jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
A wani yanayi mai kama da na jihar ta Yobe, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato, Yakubu Sanda, na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya rasa damar komawa majalisar, rahoton Channels Television.
Misis Happiness Mathew Akawu, yar takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ce ta kayar da shi a zaben da aka yi a ranar Asabar na mazabar Pengana a jihar.
Yar takarar ta jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 9,926 inda ta kayar da kakakin majalisar wana ya samu kuri'u 7,936. Shi kuma dan takarar jam'iyyar PRP ya samu kuri'u 6,721, dan takarar jam'iyyar Labour ya samu kuri'u 1,028.
Ga sakamakon zaben majalisar dokokin jiha na Pengana:
APC – 7,936
PDP – 9,926
PRP – 6,721
LP – 1,028
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng
BY ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka