PDP ta dakatar da shugabanta na kasa Ayu - isyaku.com


A ranar Lahadin da ta gabata ne jam’iyyar PDP ta sanar da dakatar da shugabanta na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, bisa zargin cin zarafin jam’iyyar. Jaridar Daily trust ta ruwaito.

 Jami’an PDP na Unguwanni na gundumar Igyorov da ke karamar hukumar Gboko a jihar Benue sun dakatar da Ayu.

 Sakatariyar jam’iyyar PDP ta yankin, Vangeryina Dooyum, a madadin Kashi Philip, wanda shi ne shugaban gundumar, ya shaida wa manema labarai a Makurdi, cewa dakatarwar da shugaban jam’iyyar na kasa ya yi ya biyo bayan ayyukan da ake zargin sa da aikatawa.

 Sakatariyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun 12 daga cikin mambobi 17 na gundumar, ta bayyana cewa an cimma matsayar dakatar da shugaban na kasa ne bayan da shugabannin suka yi nazari a kan abin da ya aikata lokacin babban zaben da aka kammala.

 Sakataren, wanda shugaban gundumar da sauran mambobin majalisar zartarwa a gefen taron manema labarai, ya karanta daga cikin sanarwar da ta sanar da dakatar da Ayu.

 “Mun lura da cewa, Dr. Iyorchia Ayu wanda shi ne shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya yi aiki don ganin rashin nasarar jam’iyyar a Igyorov Council Ward.

 “A rubuce yake cewa, shi ma ya kasa biyan kudin shiga na shekara-shekara kamar yadda sashe na 8 (9) na kundin tsarin mulkin PDP na 2017 (Kamar yadda aka gyara).

 “Bincike ya kuma nuna cewa, bai kada kuri’a ba a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

 “An kuma gano cewa, mafi yawan makusantan sa sun yi aiki da jam’iyyar adawa, APC, kuma a sakamakon haka, sun illata ayyukan PDP a Igyorov Ward.

 “Saboda abubuwan da suka gabata, mun amince da kada kuri’ar rashin amincewa da Dokta Iyorchia Ayu tare da dakatar da shi a matsayin dan jam’iyyarmu nan take.  Dakatarwar ta fara aiki daga ranar 24 ga Maris, 2023."

 Ku tuna cewa a karshen mako ne jam’iyyar PDP a matakin jiha ta kada kuri’ar amincewa da Gwamna Samuel Ortom, wanda shugaban zartarwa na kasa a matakin koli ya mikawa kwamitin ta na ladabtarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN