An sami ruwan saman farko a garin Birnin kebbi babban Birnin jihar Kebbi ranar Litinin 20 ga watan Maris.
Da farko an fara yayyafi da misalin karfe 7 na yamma, daga bisani ruwan suka ci gaba da yawa har tsawon fiye da awa daya.
Da misalin karfe 10 na dare, an sake sheka ruwan saman na tsawon kusan minti 30.
Kafin saukar ruwan saman, an yi fama da matsalar zafin yanayi Yan kwanakin baya a garin Birnin kebbi da kewaye.
BY ISYAKU.COM