Bala Ibn Na'Allah Dan takarar kujerar Sanata a mabarsa ta Kebbi ta kudu ya rasa kujerarsa bayan kammala zaben 2023.
Garba Musa Maidoki, dan takarar jam'iyyar PDP a mazabar ne ya lashe zaben da aka yi a karshen makon jiya, Daily Trust ta ruwaito.
Baturen zaben jihar, Farfesa Ibrahim Muhammad ya sanar da sakamakon zaben da cewa, dan takarar na PDP ya samu kuri'u 75,232 yayin da Na'Allah ya samu 70,785.
Na'Allah ya kasance a majalisar dattawa har sau uku, kana ya shafe majalisar wakilai ta tarayya sau biyu.
Ya rasa kujerarsa ne ga dan takarar PDP da wannan ne karonsa na farko na takara da akalla kuri'u 5000.
A bangare guda, wasu mabiya jam'iyyun siyasa a jihar Kebbi sun rike wasu jami'an zabe a mazabar sanata Kebbi ta tsakiya kan sakamakon zabe.
'Yan a mutun jam'iyyun suna ta zanga-zangar jinkirin sanar da sakamakon zaben sanatan yankin tsakanin gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Adamu Aliero.
Bayan ganawa da sanata Aliero da dan takarar gwamnan jihar, Janar Aminu Bande (mai ritaya), sun toshe mashiga filin tattara zabe na jihar Kebbi, 21st Century Chronicle ta ruwaito.
An farmaki wani jami'in INEC da ya sha dakyar, wanda rahoto yace an fitar dashi daga wurin dakyar.
Hakazalika, 'yan jaridar da ke daukar hotunan abin da ya faru a wurin, amma an samu daukin jami'an tsaro
BY ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka