Type Here to Get Search Results !

KAI TSAYE: INEC reshen jihar Kebbi ta jaye duk dama da Jami'in tattara zabe na Marafa ward B-kebbi da ya yi batan dabo yake da ita kan harkar zaben, ta nada wani


Hukumar zabe mai zaman kanta INEC reshen jihar Kebbi ta jaye duk dama da Malam Yusuf Isah Yahaya na Federal University Birnin kebbi yake da ita bayan ya yi batan dabo daga wajen zabe kuma ta nada wani don ya tattaro sakamakon zabe da aka gudanar tun ranar Asabar.

Sanarwar hukumar ta ce " Duj wata dama da aka ba Malam Yusuf ya kau, bashi da wata dama domin yin wani abu a ko Ina"

Equity FM Birnin kebbi ta labarta rahotanni na cewa Jami'in tattara sakamakon zabe na gundumar Marafa da ke karamar hukumar Birnin kebbi ya yi batan dabo tare da sakamakon zabe na gunduma ta Marafa.


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies