Hukumar ta INEC ta saki jerin sunayen rumfunan zabe 240 da ba za a yi zabe ba a kasar nan a zaben 2023.
A baya hukumar zaben ta bayyana cewa, ba za a yi zabe a rumfunan ba saboda basu da wadanda suka yi rajistan yin zabe a cikinsu.
A jerin rumfunan zaben 240 an ce ba za a yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Faburairun bana ba.
Hakazalika, hakan na nufin ba za a yi zaben gwamna na ranar 11 ga watan Maris ba da ma ‘yan majalisun jiga fadin kasar ba.
A kasa mun tattaro muku jerin sunayen rumfunan kamar haka:
Latsa nan ka karanta jerin runfunan: