Mafita ta samu: Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana mai jan hankali kan sabbin Naira na CBN

 


Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya ce tsarin sauya fasalin naira wanda ya haddasa ƙarancin takardun kuɗi ya jefa mutane cikin ƙunci da takaici. Legit.ng ya wallafa.

Sultan ya bayyana haka ne ranar Litinin a wurin taron "Farfaɗo da kiyon dabbobi da magance rikice-rikice masu alaƙa," kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sarkin Musulmin ya ce ya zama wajibi hukumomi masu ruwa da tsaki kan sabon tsarin su yi duk me yuwuwa wajen sanyaya zuƙatan mutane da wahalhalun da suka shiga.

Duk da Kotun Koli ta umarci FG ta jinkirta haramta amfani da tsoffin naira da ta tsara ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023, har yanzun ana fama da ƙarancin naira a hannu a sassan ƙasar nan.

Mai Alfarma Sarkin Musulmai ya ce:

"Mutane suna fama da yunwa, shin akwai kuɗi? Babu tsabar takardun naira. Mutane sun fusata kuma ga yunwa na damunsu, bari mu ga yadda zamu yayyafa wa yanayin nan ruwan sanyi."

Akwai bukatar kawo karshen rikicin manoma da makiyaya - Sultan

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ƙara da cewa ya kamata zaman tattaunawa irin wannan ya lalubo hanyoyi magance rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan kuma a aiwatar tun daga tushe.

A ruwayar Sahara Reporters, Sultan ya ci gaba da cewa:

"Ya kamata mu jingine siyasa a gefe, mu baiwa ci gaba muhimmanci musamman a kan gama garin mutum. Bayan turancin farfesoshi a aji, ta ya ci gaba zai kai ga talakan manomi ko Fulani wanda bai san komai ba sai kiwo."

"Na je jihar Benuwai a matsayin Sultan sau biyu muna zama da gwamnoni da Sarakuna mu tattauna hanyoyin samun zaman lafiya a jihar. Daga karshe za'a samu shawarwari amma sai mu watsar."

"Ya kamata wannan taron ya banbanta da sauran, mu nemo hanyoyin kuma mu aiwatar da su yanzu ba sai wani lokaci ba."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN