Hukumar Yan sandan jihar Kebbi ta dukufa wajen neman wasu mutane biyu da suka taushe wata yarinya suka yi lalata da ita da karfin tsiya a unguwar Badariya a garin Birnin kebbi. Shafin isyaku.com.ya samo.
Rahotanni na cewa wadanda ake nema sun yaudari yarinyar ne lokacin da take kan hanyarta na zuwa makarantar Islamiyya. Suka kai ta dakinta suka yi lalata da ita.
Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi Ahmed Magaji Kontagora ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Yan sanda a Gwadangaji ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu.
CP Magaji ya ce:
"A ranar 4 ga Fabrairu, 2023 da misalin karfe 4:15, wata Fadila Umar mai shekara 15 a unguwar Badariya, Birnin Kebbi, yayin da take kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya,
Wani Bello Shehu mai shekara 27 da abokinsa mai suna Yahaya Abdullahi, wadanda ke zaune a unguwar suka yaudareta suka shige dakinsu suka yi lalata da ita.
Yan sanda na ci gaba da nemo su bayan sun gudu sakamakon aikata laifin" . Inji CP Magaji
BY ISYAKU.COM