Dubun wani da ake zargin Dan Luwadi ne ya tonu a garin kalgo na jihar Kebbi bayan ya yi yunkurin aikata Luwadi da yaro Dan shekara 5. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Rundunar Yan sandan jihar Kebbi ta cafke shi bayan ya yi barazar cewa zai kashe yaron idan ya gaya ma wani.
Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi CP Ahmed Magaji Kontagora ya shaida wa manema labarai ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu 2023 a hedikwatar Yan sanda a garin Gwadangaji.
Kwamishinan ya ce:
"A ranar 2 ga Fabrairu, 2023 da misalin karfe 1:30 na rana wani mai suna Sani Abubakar mai shekaru 20 a unguwar Tudun Wada, cikin garin Kalgo, ya yi yunkurin yin lalata da wani yaro mai shekaru 5 da haihuwa ta duburarsa wadda ya sabawa tsarin halitta.
Ya kuma yi barazanar kashe shi idan ya kuskura ya tona asirin da ke tsakaninsu.
Za a gurfanar da wanda ake zargin a Kotu bayan an kammala bincike". CP Magaji ya ce.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI