CID sun yi wa Likitan bogi kamun kazan Kuku a Birnin kebbi jihar Kebbi


Rundunar Yan sandan jihar Kebbi ta kama wani Likitan bogi mai suna Yusuf Omotayo Abdulfatai  a garin Birnin kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Jami'an sashen leken asiri da binciken manyan laifuka na Yan sandan jihar Kebbi SCID ne suka yi ram da Omotayo a unguwar tsohon gareji ko kauyen kanikawa.

An gano cewa Omotayo Yana sojan gona da takardun bogi wai shi Likita ne da ke aiki da Asibitin DDG ne da ke Unguwar kafin ma'aikatan lafiya na jihar Kebbi su gano shi. Daga bisani suka mika shi ga Yan sanda.

Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi CP Magaji Kontagora ne ya shaida wa manema labarai ranar Litinin a  hedikwatar Yan sanda a garin Gwadangaji.


Ya ce:

"A ranar 30 ga Janairu, 2023, wani Yusuf Omotayo Abdulfatai mazauni tsohon kauyen kanikawa a Birnin Kebbi, ya shiga hannun 'yan sanda a SCID, Birnin Kebbi, daga hannun ma'aikatan lafiya ta jihar Kebbi, 

 An kama shi da takardun shaidar da ake zargin jabun takardu ne kuma yana bayyana kansa a matsayin Likitan da ke aiki da wani Asibiti mai zaman kansa mai suna DDG Medical Centre, Birnin Kebbi.  

A yayin gudanar da bincike an gano wasu abubuwa da dama da ake zargi da suka hada da takardun jabu da na bogi sannan wanda ake zargin ya amsa laifin aikata laifin.  

Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kotu". Inji CP Magaji.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN