Yan sanda sun kama Miji da yan uwasa 3 da suka yi wa dan shige wajen matarsa dukan ajali a jihar kebbi


Rundunar Yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu mutane Yan uwan juna su hudu bisa zargin yi wa wani mutum dukan ajali a karamar hukumar Ngaski. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Wanda aka kashe mai suna Yunana Ayuba ya shiga gidan wani mutum ne bayan ya baro kauyensu kuma ya shiga gidan wani mtum ya kira wata matar aure suka zagaya bayan gidan inda miji ya kama su.

Sakamakon haka ya kira yan uwansa suka yi wa Yunana duka har ya suma daga bisani ya sheka Lahira.

Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi CP Ahmed Magaji Kontagora ya shaida wa manema labarai ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu a Birnin kebbi.

Ya ce: 

"A ranar 30 ga Janairu, 2023 da misalin karfe 9 na dare, wani Yunana Ayuba daga kauyen Kyaun a karamar hukumar Ngaski, ya je kauyen Mokoto a karamar hukumar Ngaski.

Ya shiga gidan wani Yohana Musa ya kira matarsa ​​mai suna Abigail Yohana a bayan gidansa.  

Da mijin ya gan Yohana Musa tare da matarsa, ya kira ‘yan’uwansa, wato;  Bawa Yawai, Solomon Moses da Luka Musa suka bi su suka yi wa Yunana Ayuba duka har ya suma.  

Bayan samun rahoton ne aka tattaro tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, inda suka dauke wanda abin ya shafa, aka garzaya da shi babban asibitin Warrah, inda wani Likita ya tabbatar da mutuwarsa.  

Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban Kotu". Inji CP Magaji.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN