Dubun mutanen ua cika ne a garin Warrah da ke karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi.
Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi Ahmed Magaji Kontagora ya sanar wa manema labarai a garin Birnin kebbi ranar 20 ga watan Fabrairu.
Ya ce:
" Jami’an ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Warrah tare da taimakon kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) a tashar mota ta Warrah ranar 29/01/2023.
Sun kama wasu mutane 3 dauke da takardun kudi na kudi naira miliyan goma sha bakwai. (N17,000,000), wanda ake zargin jabun ne.
Wadanda ake zargin su ne: Faruku Zubairu (2) Ibrahim Musa da (3) Salisu Mohammed duk na kauyukan Gungun Tawaye da Chupamini, a karamar hukumar Ngaski.
An kammala bincike kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Kotu".
BY ISYAKU.COM