'Yan daba sun farmaki matar Gwamna a jihar arewa, sun fasa kan daya daga cikin 'yan tawagarta

 


Yola, Adamawa - 'Yan daba a ranar Asabar sun farmaki tawagar matar gwamnan jihar Adamawa, Lami Ahmadu Fintiri. Rahotun legit.ng.


'yan sanda

'Yan Daba Sun Kaiwa Matar Gwamnan a Arewa Farmaki, An Halaka Mutum 1. Hoto daga Thecable.ng Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin a takardar da ya saki ga manema labarai a Yola ranar Lahadi.


DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka


Yace an kai farmaki kan tawagar motocinta ne a garin Muchala da ke yankin Mubi inda wasy bata-gari suka dinga jifansu yayin da suka shiga wani kauye halartar taron matan Katolika.


'Yan daban da ke dauke da duwatsu da sanduna sun ragargaza mota kirar bas mai mazaunin mutum 18 da ke dauke da manema labarai kuma sun rauna wani mutum daya mai suna Dauda, Daily Trust ta rahoto.


Daya daga cikin wadanda ke cikin tawagar da baya so a kira sunansa saboda bashi da damar tattaunawa kan batun, ya sanar da Daily Trust cewa matar Fintiri bata samu rauni ba kuma bayan nan ta koma Yola yayin da Dauda da ya samu a rauni a kai yake samun sauki.


Takardar da 'yan sandan suka fitar ta ja kunnen masu tada fitina kan cewa ba za su ci banza ba saboda rundunar ta shirya tabbatar da zaman lafiya a jihar inda ta kara da cewa an aike jami'ai don cafko maharan.


Nguroje yace kwamishinan 'yan sandan jihar, SK Akande, ya aike da jami'ai daga rundunar SRRT don dakile abinda ka iya tasowa tare da cafko bata garin.


An gano cewa, soyayyar shan minti suke yi kuma ya raba shi da kanwarsa amma ya ki ji, lamarin da yasa ya dauka hukunci a hannnunsa bayan da ya kama su dumu-dumu.


Daga shafin isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN