Dambe ya kaure tsakanin yan mata 2 a gidan saurayi bayan sun kai masa ziyarar bazata

 


Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Juwon ta labarta yadda aka ba hammata iska ranar zagayowar haihuwar saurayinta yayin da ta iske shi tare da wata budurwa. Legit.ng ya wallafa.


Budurwar mai shekaru 21 ta bayyana yadda ta shirya wa saurayin nata bikin zagayowar ranar haihuwarsa a matsayin ba-zata inda ta yi hayar mai busa algaita da kyautuka, ga mamakinta ta iske wata budurwa a gidan shi tana shirya mishi irin abun da ta shirya.


Take a nan 'yan matan suka kwashi dambe a gidansa, wanda ya yi sanadiyyar samun raunin daya daga cikin masu busa algaitar da suka zo da su.


Abun mamaki shi ne yadda suka gano babu wacce yake so da gaske a cikin su biyun.


A cewar Juwon:


"Na bukaci mai busa algaita ya taimaka min don ba saurayi na mamaki ranar zagayowar haihuwarsa. Ni da wata yarinya muka je tare da wasu daban don bashi mamaki.


"Hakan ya yi sanadiyyar samun raunin daya daga cikin masu busa sarewar. Daga karshe dai mu biyun mun gano yaudararmu yake."


Daga ganin kudin ta nufi caji ofis da su inda aka nemo masu kudin. Ashe wasu ma'aurata ne aka basu matsayin gudumawa na aurensu amma suka yadda.


Tuni 'yan sandan suka kafa gidauniyar taimakon matar wacce za a hada mata kudin da za ta siya motar kanta da shi.


A halin yanzu an hada mata kudin da suka kai $25,000 daga cikin $45,000 da ake fatan hadawa.

Daga isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN