Da dumi-dumu: Manyan jihohin arewa 3 sun maka Buhari, Emefiele da CBN a Kotu kan karancin Naira

 


Wasu jihohin arewa uku sun juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya kan manufarsa na sauya takardun naira inda suka maka shi a kotun koli. Legit.ng ya wallafa.


Channels TV ta rahoto cewa jihohin na arewa da suka hada da Kaduna, Kogi da Zamfara sun nuna damuwarsu kan illar da ke tattare manufar sauya kudi na babban bankin Najeriya ya jefa mutane inda suka bukaci kotun kolin da ta dakatar da aiwatar da shi.


Buhari da gwamnonin Kogi, Zamfara da Kaduna


Jihohin arewa 3 sun maka Buhari a kotu

A cikin karar da suka shigar ta hannun lauyansu AbdulHakeem Uthman Mustapha (SAN), jihohin sun bukaci kotun da ta dakatar da gwamnatin Buhari da ta dakatar da jami'anta daga aiwatar da shirin.


Saboda haka, jihohin na arewa uku suna so kotun ta hana gwamnatin tarayya aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 a matsayin kudin kasar.


Jama'a na fuskantar matsi na rashin sabbin kudi

Masu shigar da karar sun ce tun bayan sanar da manufar, ana fuskantar karancin sabbin kudi a Kaduna, Kogi da Zamfara, suna masu cewa al'ummar da suka shigar da tsoffin kudadensu a banki suna fuskantar matsin rayuwa.


Aun kuma bayyana cewa yawansu sun rasa hanyar samun sabbin kudi don gudanar da harkokinsu na yau da kullun, rahoton The Cable.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN