'Yan bangar siyasa sun sace na’urar tantance masu zabe ta BVAS guda takwas. Shugaban Hukumar Zabe ta Kasar (INEC) Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar dachaka.
Ya ce an sace na’urorin ne a Jihohin Katsina da Delta, Kodayake ya ce jami'an tsaro sun sami nasarar kwato guda uku daga ciki.
Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na farko kan zaben na ranar Asabar.
Sai dai Farfesa Mahmud ya ba dukkan wadanda ke kan layi tabbacin cewa za su sami damar kada kuri'arsu, ko da bayan cikar wa'adin karfe 2:30.
Daga Abbas Jimoh da Sani Ibrahim Paki na Jaridar Aminiya.
BY ISYAKU.COM