Rahotanni daga jihar Kogi na cewa wani matashi mai suna Akayama a yankin Anyigba da ke kamaramar hukumar Dekina ya mutu bayan yan bindiga sun bindige shi .
Wau yan daba da suka farmaki garin don sace kayan zabe ne suka bindige matashin har lahira, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Lamarin ya afku ne da misalin karfe 11:00 na safiyar yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu inda ake gudanar da zaben shugaban kasa a fadin kasar. Legit Hausa ya wallafa.
Yan daban sun mamaye garin suna ta harbi kan mai uwa da wahabi sannan suka dungi sace kayan zabe daga mazabu daban-daban.
An harbe maarigayin wanda mazauna yankin suka yi ikirarin cewa ya kammala karatunsa a bangaren ilimin tattalin arziki a jami'ar Prince Abubakar Audu, Anyigba, a wata rumfar zabe da ke in Iji-Anyigba.
Lamarin ya hargitsa zaben da ke gudana a garuruwan Dekina, Agbeji, Ajiolo, Abejukolo da Ejule yayin da yan daba suka kwace rumfunar zabe, suna kora masu zaben da basa biyayya ga wata jam'iyya.
A halin yanzu, an ce an tura sojoji domin su dawo da zaman lafiya a yankin.
INEC ta soke zabe a rumfunar zabe 7 a yankin Kogi ta gabas
A halin da ake ciki, jaridar Vanguard ta rahoto cewa an soke tsarin zabe a rumfunar zabe bakwai a yankin Kogi ta gabas.
Yayin da aka soke zabe a rumfunar zabe biyu a Anyigba, karamar hukumar Dekina, sauran rumfuna biyar da aka soke zaben sun kasance a yankin Omala ta jihar Kogi.
Daya daga cikin rumfar da aka soke ita ce rumfar 01, gudunmar Abejukoli da ke karamar hukumar Omala.
BY ISYAKU.COM
To Allah ya jikansa ya sa a gama zabe lafiya
ReplyDeleteWai yandaba su kashe mutum a wajen zabe Kuma jami'an tsaro basu kamasu ba
ReplyDeleteKo ku kashekowa dakowa Atiku ne sugabankasa
ReplyDeleteRubuta ra ayin ka