Ta bayya: Manyan Sarakunan Yarabawa 7 sun bayyana wanda za su goyi bayansa a zaben shugaban kasa 2023


Rahotanni na cewa Gamayyar sarakunan Yarabawa sun dunkule suka hada kai tare da goyon bayan dan takarar shugabancin kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga Fabrairu. Legit.ng ya ruwaito.

Sarakunan Yarabawan da suka fito daga jihohin Ekiti, Lagos, Kogi, Kwara, Ogun, Ondo, Osun, da kuma Oyo, sun bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da suka fitar bayan tattaunawar da su ka gudanar a dakin taro na International Conference Centre, da ke jami'ar Ibadan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ooni na Ife da sauran sarakunan Yarabawa suna fatan ganin Bola Tinubu ya gaji kujerar shugabancin kasa.

Legit.ng ta ruwaito cewa sarakunan sun gamsu da manufofin da Tinubu ya gabatar a lokacin tattaunawar. Kusan gaba daya sarakunan kasar Yarabawa, Kwara da Kogi gaba daya sun amince da takarar tsohon gwamnan na Jihar Lagos.

Shugabancin kasa na 2023: Abin da yasa muka goyi bayan Tinubu - Sarakunan Yarbawa
Sarakunan Yarabawan sun amince da cewa Tinubu ya fi duk sauran cancanta da ya gaji kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya.

Sarakunan sun gamsu da Tinubu ''da irin gudunmawar da ya bawa dimukradiyya da kuma irin rawar da ya taka don cigaban dimukradiyya a Najeriya.''

Wani sashi na labarin ya bayyana cewa:

''Abu ne a bayyane muna goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu saboda irin kyakkyawan tarihi da kuma irin muhimman abubuwan da ya cimma wanda ya sa ya hau saman sauran yan takarar a matsayin wanda kadai zai iya kawa hadin kai, daidaito da adalci ga tsarin Najeriya."


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN