An kashe Mista Oyibo Chukwu dan takarar Sanata na Mazabar Inugu ta gabas a jam'iyyar LP kwana biyu kafin zabe.
Tashin-tashina na ci gaba da kamari a yankin Kudu Maso Gabas duk da karatowar babban zaben 2023. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
An ruwaito cewa sai da maharan suka harbe dan takarar, sannan suka kone shi tare sa magoya bayan nasa a cikin mota a yankin Amechi a Karamar Hukumar Awkunanaw yayin da yake dawowa daga yakin neman zabensa.
Dan takarar gwamnan jihar a Jam’iyyar LP, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce ana yi wa ’ya’yan jam’iyyarsu barazana saboda yadda suke kara samun kwarin guiwar takara.
Sai dai har yanzu rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da kisan dan takarar ba.
Mahara sun lashi takobin hana yin zabe a yankin amma jami’an tsaro sun bayar da tabbacin bayar da tsaron da ya dace don gudanar da zaben 2023.
BY ISYAKU.COM