Siyasar Kebbi: Yadda Dan Bagudu ya shara wa al'ummar Masarautar Zuru karya a lokacin taron yakin neman zabe a garin Ribah

 


An zargi gwamna Abubakar Atiku Bagudu da shara wa al'ummar Masarautar Zuru karya a garin Ribah.


Malam Sanusi Ahmadu ya ce " Gwamna yazo garin Ribah ya shara mana karya cewa zai yi hanyar Ribah zuwa Zuru.


A kasa da wata hudu zai yi aikin da ya kasa yi tsawon shekara kusan 8 ? Kowa ya san cewa wannan yaudar ne kawai.


Zance samar da tsarin sarrafa rogo domin samar da man fetur, ka san Bagudu karya ne kawai ya shara wa jama'a da sunan yakin neman zabe. Tun yaushe yake zancen man fetur daga rogo? Mi ya sa bai yi ba sai saura yan watanni ya sauka daga mulki zai kawo mana zancen yaudara?.


Kan harkar tsaro ai kowa ya san ya gaza, domin yanayin tsaro na garin Ribah da Masarautar Zuru ya tabarbare fiye da yanayin tsaro da Bagudu ya samu a 2015 kafin ya zama Gwamna an fi samun tsaro a Masarautar Zuru bisa ga wannan irin wulakanci da jama'a suka gani a Masarautar Zuru da sunan ana kokari kan harkar tsaro" inji shi.


"Abin  da ya kamata al'umma su tambaya kafin su yi zabe shine". 


"Me  ya sa Bagudu ya ki sa baki a kammala hanyar Dabai zuwa Koko duk da yake hanyar Gwamnatin Tarayya ne. Amma zai iya neman alfarma domin a kammala hanyar kafin karshen mulkinsa".


"Dakarkari  nawa ke tsare a gidan yari a Birnin kebbi, kuma a bisa wane laifi?"


"Mutum  nawa Yan bindigan suka kashe a Masarautar Zuru tun daga 2015 zuwa yau".


Bincike ya nuna cewa Gwamna Bagudu baya son a wallafa barnar da Yan bindiga ke yi wa jama'a a Masarautar Zuru a jaridu da kafofin watsa labarai da sunan tsarin tsaro, Amma ana fitar da miliyoyin naira da sunan gudanar da harkar tsaro a Masarautar da kudancin jihar Kebbi. 

3 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. gaskiya akwai abin bakin chiki ache shakara takwas ba wani abin abin amfani daya da za'a gwadi ache gashi anyi muna,ba agehen ilimi ba ba a lafiya ba hayaba, kaidai allah yasauwaka

    ReplyDelete
  2. hmnnn mutnen Zuru ku yi hkuri

    ReplyDelete
  3. Humm mutane Ribah har sunga wurin sauraron kamfe, talakawa dai basuda basiru wasun sun, ana kashe Ku ana zuwa ana zura maku karya da yaudara.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN