![]() |
Illustrative picture |
Rahotanni na cewa babu wani dan bindiga da jami'an tsaro suka kashe a yankin jihar Kebbi cikin yan kwanakin nan.
Wasu rahotannin daga majiyoyi da dama na cewa jami'an tsaro sun yi artabu ne da yan bindiga a yankin Zamfara ba a yankin jihar Kebbi ba yan kwanakin da suka gabata.
Wannan na zuwa ne bayan jita-jita ya kaure a Masarautar Zuru cewa an kashe dukkan yan ta'addan da ke addabar yankin Kanya da sassan karamar hukumar Danko Wasagu.
Rahotun na cewa an ga mota makare da babura da sauran kayaki wadanda ake zargin na yan bindigan ne.
Lamari da ya sa wasu Yan siyasa suka fara yada jita jita domin alakanta lamarin da nasara da suka gaza samu a Masarautar Zuru tun 2015.
Yanzu dai ta tabbata cewa karya ne zancen kashe yan bindigan a Masarautar Zuru da kewaye.
Gwamnatin jihar Kebbi na kashe miliyoyin kudin jama'ar jihar Kebbi da sunan tafiyar da harkar tsaro a Masarautar Zuru. Sai dai tun 2015, har zuwa wannan lokaci ta kasa samar da tsaron da take ikirarin fitar da miliyoyin naira domin tafiyarwa a Masarautar Zuru.