Abuja - Hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa (NUC) ta umarci a rufe jami'o'i a dukkan sassan ƙasar nan domin baiwa ɗalibai damar ba da gudummuwarsu a babban zaɓen 2023. Legit.ng ya wallafa.
Rahoton Punch ya nuna cewa a wata wasika da aka aike wa shugabannin jami'o'i (VC) da Daraktoci, NUC ta bayyana cewa wannan umarnin ya fito ne daga Ministan ilimi, Adamu Adamu.
A matsayin shugabannin jami'a (VC) kuna da masaniyar cewa babban zaben 2023 zai gudana ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, na shugaban ƙasa da majalisun tarayya da 1 ga watan Maris, 2023 na gwamna da majalisar dokoki."
"Duba da halin da ake ciki da tsaron ma'aikata, dalibai da kyayyakin makarantu, Ministan ilimi, Mal Adamu Adamu, ya umarci jami'o'i da Cibiyoyin jami'a su tafi hutu tsakanin 22 ga Fabrairu da 14 ga watan Maris, 2023."
Saboda haka, ana umartar VC da daraktoci su rufe makarantunsu daga ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu, 2023 zuwa ranar Talata 14 ga watan Maris, 2023."
- A cewar wasikar da NUC ta aike wa mahukuntan jami'o'i.
Bugu da kari, rahoton Daily Trust yace wasikar ta kara sabunta tabbacin babban Sakataren NUC, Farfesa Rasheed Abubakar, yayin da ya gode wa shugabannin jami'o'i bisa fahimta da kuma haÉ—in kan da suka bayarwa.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa 'yan Najeriya sun yi ta kiraye-kirayen gwamnati ta ba da hutu a manyan makarantu domin É—alibai su samu damar kaÉ—a kuri'a a zabe mai zuwa.
A bayanan da hukumar zabe ta ƙasa INEC ta fitar, dalibai sama da miliyan 26m ne suka yi rijistar zabe a Najeriya.