Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi na kasa a ranar 16 ga Fabrairu, 2023 da karfe 7.00 na safe. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba.
Don haka Adesina ya bukaci gidajen Talabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su hada kai da gidajen Talabijin na Najeriya da Rediyon Najeriya domin yada shirye-shiryen.
Rubuta ra ayin ka