Da dumi-dumi: Buhari zai tsawaita wa’adin tsofaffin kudi zuwa watan Afrilu


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na duba yiwuwar tsawaita wa’adin tsofaffin takardun kudi da kwanaki 60. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Wannan dai a cewar wani rahoto da jaridar The Cable ta wallafa, wani yunkuri ne na kaucewa bijire wa umarnin Kotun Koli da ta ce tsofaffin takardun kudin na N1000, N500 da N200 su ci gaba da aiki har sai ta yanke hukunci.

Hukuncin na wucin-gadi da Kotun Kolin ta yanke na zuwa ne bayan karar da wasu gwamnoni suka shigar suna kalubalantar matakin kawo karshen wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin.

A halin yanzu dai Babban Bankin Najeriya CBN ya ce yana kan bakansa na cikar wa’adin tsofaffin takardun kudin a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Sai dai wani kusa a gwamnati, ya shaida wa Jaridar The Cable cewa Buhari ya damu da halin kunci da ’yan Najeriya suka tsinci kansu sanadiyyar karancin takardun kudi, lamarin da zai tsawaita wa’adin tsofaffin takardun kudin zuwa 10 ga watan Afrilu.

Haka kuma, majiyar ta ce Shugaban Kasar na nazari a kan abin da zai biyo baya muddin aka bijire wa umarnin Kotun Kolin da ke da ta cewa kan duk wata doka da Kundin Tsarin Mulki.

A cewar majiyar, an tattauna wannan batu ne yayin ganawar Shugaba Buhari da Shugabannin Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) da kuma Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC a safiyar wannan Larabar.

A bisa wannan nazari da duba yiwuwar tsawaita wa’adin tsofaffin takardun kudin da Shugaban Kasar ke shirin yi, ana kuma tsammanin gwamnoni za su janye karar da shigar a gaban Kotun Kolin.

“Wannan ita yarjejeniyar da aka kulla domin bai wa Shugaba Buhari damar tsawaita wa’adin sannan kuma a sanar da matakin a hukumance,” inji majiyar.

“Akwai yarjejeniyar bayar da damar ci gaba da hada-hada da tsofaffi da sababbin takardun kudin a lokaci guda nan da zuwa kwana 60 masu zuwa.

“Sai kuma yarjejeniyar da ta kayyade cewa duk wata tsohuwar takardar naira da ta shiga banki ta shiga ke nan har zuwa lokacin da sabbin takardun kudin za su wadata.”

Majiyar ta ce kusan duk bangorin sun amince da wannan mataki na Shugaba Buhari face Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna da ya hau kujerar naki ta dole sai an soke sabon tsarin kudin da CBN ya kawo.

Bayanai sun ce Buhari wanda ya yi jinkirin shiga zaman Majalisar Zartarwa da kusan minti 40 a safiyar wannan Larabar, ya gana da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da kuma Darektan Hukumar Kula da Hada-Hadar Kudi (NFIU), Modibbo Tukur kan bukatar tsawaita wa’adin tsofaffin takardun kudin.

Majiyar ta ci gaba da cewa, Buhari ya yanke wannan shawara ce domin rage radadin da al’ummar kasar ke fuskanta sanadiyyar sabon tsarin na kudaden kasar.

“Buhari ba zai bijire wa umarnin Kotun Kolin ba, amma ya damu matuka kan halin kunci da al’ummar kasar nan suka shiga.

“An kuma gano cewa akwai wasu manyan kasar da ke take-taken tunzura al’umma a yayin da duk rintsi suna da hanyoyin samun sabbin takardun kudin alhali talakawa na fama saboda ba su da irin wannan damar.

“Saboda haka Buhari ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen warware wannan tankiya,” a cewar majiyar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN